Muryar Amirka ta cika shekaru saba'in da kafuwa

Bikin cika shekaru saba'in da kafuwar Muryar Amirka

A ranar daya ga watan Fabrairun alif dari tara da arba'in da biyu, kusan watani biyu bayan da kasar Japan ta kaddamar da hari akan tashar jiragen ruwan Pearl Habour,, dalilin daya sa Amirka ta shiga yakin duniya na biyu ne, Muryar Amirka ta fara watsa shirinta na farko.

Muryar Amirka tana bikin cika shekaru saba'in da kafuwa.

A ranar daya ga watan Fabrairu alif dari tara da arba'in da biyu Muryar Amirka ta fara gabatar da shirinta na farko. Ta gabatar da shirin ne kusan watani biyu bayan da kasar Japan ta kai hari kan tashar jiragen ruwan Pearl Habour, dalilin daya sa Amirka ta shiga yaki duniya na biyu.

Dan Jarida Harlan Hale, shine ya gabatar da shirin Muryar Amirka na farko cikin harshen Jamusanci daga birnin New York daga gidan rediyo mai cin matsakaicin zango

Harlan Hale, yace wannan Muryar ce kuke sauraro daga Amirka. Kullu yaumin a daidai wannan, zamu gabatar muku da shiri akan ra'ayin Amirka gameda wannan yaki. Kila labari ne mai dadin ji ko kuma mara dadain ji, amma zamu yi kokarin mu fada muku gaskiya komai dacinta.

Direktan Muryar Amirka David Ensor, yace har kwana gobe wadannan kalamai suna da muhimmanci, kuma sune suke yiwa Muryar Amirka jagoranci.

Tu dai lokacinda aka kafata a alif dari tara da arba'in da biyu, Muryar Amirka ta fadada kafofin yada labarunta a farnoni dabam dabam, wadanda mutanen da aka kiyasta sun kai miliyan dari da arba'in da daya suke sauraro da kalo a kowane mako.

Yanzu haka Muryar Amirka tana gabatar da shirye shirye cikin harsuna arba'in da uku, kuma tana tuntunba da yin cudanya masu sauraronta ta gidajen rediyo da talibjin da kuma yanar gizo, wato Internet.