Mutane Akalla 37 Sun Mutu a Hatsarin Mota a Jihar Neja - 8/03/14
Mutane a wurinda babbar motar daukar mai tayi hadari a Fatakwal. Ranar Alhamis 12 Yuli 2012
Motar da ta yi hatsarin tana dauke da shanu da kuma mutane har 78 a lokacin da ta yi hatsari kan wata gada
WASHINGTON, DC —
Mutane akalla 37 sun rasa rayukansu a lokacin da wata motar daukar shanu ta yi hatsari a kan wata gada a Mariga dake jihar Neja.
Wasu mutanen su akalla 30 su na babban asibitin Kontagora, inda ake jinyar raunukan da suka samu a wannan hatsari.
Rahotanni na cewa wannan motar daukar shanu, tana dauke da mutanen da yawansu ya kai kiamnin 78, kuma ta fito ne daga Jihar Zamfara a kan hanyarta ta zuwa Lagos.
Ga Mustapha Nasiru batsari da cikakken bayani.
Your browser doesn’t support HTML5
Mutane Akalla 37 Sun Mutu a Hatsarin Mota a Jihar Neja Yau Jumma'a - 2'32"