Mutane kalilan suka halarci wurin bukin da aka gudanar a ofishin jakadancin Najeriya na Amurka dake Washington, DC, a yau talata, domin nuna goyon bayan shugaba Goodluck Jonathan a yayin da ya ayyana aniyar sake tsayawa takarar kujerar shugabancin Najeriya.
Akasarin wadanda suka halarci wurin wannan bukin, ma'aikatan ofishin ne tare da wasu abokansu kalilan, sai kuma shugabar jam'iyyar PDP reshen Washington, DC, Madam Arinola Awosika, wadda ta yi ikirarin cewa shugaba Goodluck Jonathan ya taka rawar gani, kuma ya cancanci sake tsayawa takara.
An saka wani makeken akwatin telebijin, inda mutane kimanin 40 zuwa 50 da suka halarci wannan gangami suka kalli shugaban yana bayyana aniyarsa daga Abuja.