Duk da kasancewar matsalolin tsaro da al’umar jihar Borno ke fama dashi, musammam ma na hare-haren ‘yan bindaga, da yanzu haka yasa mutane dayawa ‘yan gudun hijira daga kananan hukumomi da dama zuwa babban birnin Maiduguri.
Ma zauna garin dai sunce a shirye suke da gudanar da zabubbuka duk kuwa da wannan kalubale, hakan yazone bayan kwana guda da taron da aka gudanar a babban birnin Abuja, na masu ruwa da tsaki kan harkokin kasar, wanda aka mikawa hukumar zabe mai zaman kanta wuka da nama, da taje ta duba lamarin na cewar za’a iya yin zaben ko baza’a iya ba.
Sai dai al’umar jihar Bornon na ganin cewar su kan lokaci yayi, da za’a ce ambasu damar gudanar da wannan zabe duk da kuwa tashe tashen hankula da suke fama da shi.
A yanzu haka dai fiye da rabin al’umar dake jihar Borno, suna zama ne a sansanin ‘yan gudun hijira a cikin garin Maidugurin, wanda wannan shine lamarin da yafi daukar hankulan jama’a musammam ma na yiwuwar gudanar da zabe a sansanin ko kuwa.
Wakilin mu Haruna Dauda, yaji ra’ayin mutanen jihar Borno da dama wanda suke fama da wannan kalubale game da wannan zabe da ake sa ran yi a ranar sha huda ga wannan watan. Inda mutane dayawa suka shaida masa cewar a shirye suke da suyi zabe ranar sha hudu ga wannan watan.
Koma mai ake ciki ranace kawai zata tabbatar da yiwuwar wannan zabe da yanzu haka ake cigaba da mahawara na gudanar da zaben ko kuma akasin haka.
Your browser doesn’t support HTML5
Mutanen Maiduguri A Shirye Suke Da Zabe - 3'03"