Mabiya addini kirista, a jihar Gombe sun gabatar da adu’ar samun zaman lafiya, a sabuwar shekara ta 2015.
Shugaban mabiya, addini kirista, a jihar, Rev. Abari Kalla, shine ya jagoranci mabiya zuwa fadar, Gwamnatin jihar.
A jawabin maraba Gwamna Ibrahim Dankwambo, ya bayyana farin cikin sa da yanda ake samun Karin dankon zumunta tsakanin mabiya addinai daban-daban a jihar ta Gombe.
Shima shugaban na kiristocin jihar Gombe, Rev. Abari Kalla, yace mutunta juna tsakanin Musulmi da Kirista ,a jihar Gombe, shi ya kawo Karin fahimtan juna da wanzuwar zaman lafiya, a tsakanin mabiya addinan biyu.
Ya kuma kara da cewa makasudin zuwan su gidan Gwamnati, shine don yin adu’a a bisa alada, da kuma yiwa Gwamnati godiya, don yanda take rike jama’a.
Your browser doesn’t support HTML5
Adu'ar Zaman Lafiya - 3'02"