Najeriya ba zata girgiza
Shugaban hukumar Kwastam Abdullahi Dikko Inde, shine ya bayyanawa manema labaru haka a Abuja a lokacin da hukumarsa ke bukin cika shekara ‘daya da kirkiro sabon tsarin karbar haraji a tashoshin jiragen ruwa dana sama a Najeriya.
Bayan da hukumar Najeriya, ta ba hukumar Kwastam damar karbe aikin nan da ‘yan kwangila keyi na tara haraji domin Najeriya. Shirin da ya kawo cece kuce a lokacin da aka karbeshi daga hannun ‘yan kwangila.
Shugaban hukumar Kwastam din Abdullahi Inde, ya bayyana cewar hukumar Kwastam din tayi tarihi na tara harajin daya kai Naira Biliyan sau Biliyan wato Tiriliyon daya kennan na Naira a karshen wannan shekarar da ake ciki.