Najeriya ta ci alwashin rage macen macen kananan yara

Wani karamin yaro

Mahalarta taron koli kan shawo kan mace macen kananan yara sun lashi takobin hada hannu domin cimma wannan burin.

Mahalarta taron koli kan shawo kan mace macen kananan yara sun lashi takobin hada hannu domin cimma wannan burin.

Taron da Ma’aikatar lafiya ta Tarayyar ta shirye tare da hadin guiwar cibiyar lafiya matakin farko, da kungiyar likitocin kananan yara- IVAV, da kuma sauran kungiyoyin agaji na kasa da kasa, ya hada kan manyan jami’an gwamnati da shugabannin ma’aikatu da na cibiyoyi masu zaman kansu, wadanda suka taru domin hada hannu a yunkurin samar da magungunan rigakafi a kasar baki daya. Wani mataki da ake gani zai tamaka wajen rage mutuwar kananan yara a kasar da ta kasance ta biyu a duniya da ake rasa rayukan kananan yara.

Najeriya ta dauki matakai dabam dabam a lokutan baya, na shawo kan mace macen kananan yara, da suka hada da kara azama a yaki da zazzabin ciwon shan inna da tetanus da sauran cututuka da suke katse hanzarin kananan yara.

Duk da wannan yunkurin, har yanzu, akwai sauran aiki a gaba , kasancewa kananan yara da dama suna ci gaba da rasa rayukansu sakamakon kamuwa da cutukan.

Binciken na nuni da cewa, kara yawan allurar rigakafin da ake yi a halin yanzu zuwa kashi 90% zai iya ceton rayukan kananan yara dubu dari shida a Najeriya cikin shekaru goma masu zuwa , ya kuma bunkasa tattalin arzikin kasar da dala biliyan goma sha bakwai.