Najeriya ta sha Tsallake Siradin Guguwar Fitina

Jama'a a Taron Siyasa

Fargabar yuwar samun fitina a yayin zaben watan gobe, ko kuma bayan bada sanarwar sakamakon, na fitowa ne daga bakin ‘yan siyasa, da magoya bayan su, sai dai wasu na ganin wannan harsashe na da illar gaske.

Sai dai dan takarar Gwamna na jam’iyyar PDM, a jihar Taraba Barrister Kabiru Dodo, na ganin cewa Najeriya, ta sha tsallake siradin guguwar fitina.

Ya kara da cewa” Wannan al’ada ce ta Dan Adam, yana tsoron abun da bai shirya masa ba, yana kuma iya jin tsoron abunda ya shirya , a can baya anyi irin wannan harsashen a 2003, an ce idan akayi zabe Najeriya, zata rabu 2007, da 2011 ma an ce haka, amma duk anyi an waste babu abunda ya faru, akwai mutane masana daga jami’oi, da masu yin ba’asi, akan al’ammuran dake tafiya a duniya, sun yi Magana a 2003, cewa lallai, Najeriya zata rabe amma bamu rabe ba, mu mutanen Najeriya, idan ba don an hana mu samu shugabanci yadda yakamata ba, babu wata kasar da zaka je ka ji dadin zamanta kamar Najeriya.”

Your browser doesn’t support HTML5

Zaben Najeriya - 2'44"