Duniyar Mu Cikin Hotuna A Yau Talata 17 Nuwamba 2015

Fasinjoji su na kokarin tserewa ta gefen wani jirgin ruwan jigilar fasinja mai suna KM Wihan Sejahtera bayan da ya tuntsure a tashar jiragen ruwan Tanjung Perak, Surabaya, Java ta Gabas.

Jama'a sun hallara a dandalin Capitol Square na birnin Toulouse, dake kudancin Faransa, domin karramawa da jimamin mutanen da aka kashe ko aka raunata a hare-haren Paris.

'Yan sanda dauke da makamai a kofar filin wasa na Wembley dake London, kafin wasan kwallon kafa na sada zumunci a tsakanin Ingila da Faransa.

Wata mata tana wucewa karkashin tutar Amurka da aka sauko da ita kasa a jikin Hasumiya ta Kasa ta Amurka dake tsakiyar birnin Washington DC, domin karrama mutanen da aka kai ma farmaki a birnin Paris.

A karon farko, gidan ajiye dabbobi na kasa dake Kuala Lumpur a kasar Malaysia, ya nunawa duniya wata jaririyar Panda mai wata 3 da haihuwa a sashe na musamman da aka kebe don goyon irin wannan dabba dake fuskantar barazanar karewa a duniya.

Magoya bayan Hong Kong su na dauke da kwalayen nuna bijirewa a wasan kwallon kafa na share fagen shiga gasar cin kofin duniya ta 2018 da aka buga tsakanin Hong Kong da China a tsibirin na Hong Kong.

Hotuna daga kowace kusurwa ta duniya a yau talata 17 ga watan Nuwamba 2015.