Rasha ta kai hare-haren sama a birnin Zhytomyr na Ukraine

Your browser doesn’t support HTML5

Zhytomyr, shi ne birni na baya- bayan nan da Rasha ta far wa, bayan da mazaunansa suka sha lugadan wuta daga jiragen sama da daddare, lamarin da ya sa masu ayyukan gaggawa suka dukufa wajen lalube a baraguzai da kashe wutar da ta tashi a wani gida.

Zhytomyr, shi ne birni na baya- bayan nan da Rasha ta far wa, bayan da mazaunansa suka sha lugadan wuta daga jiragen sama da daddare, lamarin da ya sa masu ayyukan gaggawa suka dukufa wajen lalube a baraguzai da kashe wutar da ta tashi a wani gida. Rasha ta doshi rana ta bakwai kenan da kaddamar da wadannan hare-hare, inda ta yi biris da kiran da Shugaba Volodymry Zelenskyy ke yi na a ajiye makamai.