Yankin Wukari a cikin jihar, Taraba yayi Kaurin suna wurin tashe-tashen hakula kawo daga rikicin addini zuwa na kabilanci, amma a wannan karon wani sabon salo abun ya dauka.
Inda aka yi kwanton bauna aka kaiwa wasu mutane da suke kan hanyarsu ta tafiya daga Wukari zuwa Ibi, kamar yanda zaku ji a wannan rahoton da wakilin mu Ibrahim Abdulazeez, ya aiko ma.