Shekaran zabe a Najeriya, na cike da bayanai alkawuran da ‘yan siyasa, kan yi na in a zabe su, zasu aiwatar.
Abun da yafi bada mamaki, shine hatta ‘yan takaran da Gwamnatin tarayya, ko ta jihar ta tsayar, zaka ji suna cewa zasu kawo sauyi daga wadanda suke sun gada.
Amma kalilan ne ke cewa zasu dora daga inda na jiya suka tsaya.
Alkawuran da ake yi yanzu bayan wannan demokradiyar,ta Najeriya, tayi kusan shekaru16, basu wuce shinfida tituna, samar da ruwan sha, ko magani a asibiti, ba.
Abun da za’a ce ya karu shine, alkawarin dakatar da zubar da jinni, da hasarar dukiyoyin jama'a, ba’a bisa hakkin sharia ba.