Wani Matashi Tijani Adamu, mai sana'ar gyaran kwamfuta, yayi tir da Matasa masu zaman dumama kujera.
Matashi ya furta haka ne a wani hira da yayi da wakiliyar Dandalin Voa , Baraka Bashir. inda yace "Jama’a maza da mata mu tashi tsaye, don barci ba namune ba".
Matashi yace kira ya zamo wajibi masamman ganin yanda wasu matasa ke kashe kwana suna dumama kujera , Wannan bawan Allah dai bayan gyaran kwamfuta yana koyar da yara matasa don dogaro da kai.
Wani abun sha’awa a nan shine, yakamata a ce yara mata ma sun sa kansu a cikin irin wannan sana’ar don ba wai sana’ar maza ce kawai ba. Abu ne me kyau ga kowa ya zamo yana iya dogaro da kai ba wai sai aikin gwamnati kadai ba.