Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi na Biyu ya Soki Lamirin Auren Dole

Sarkin Kano Malam, Muhammadu Sanusi,na biyu

Mai martaba sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi, Na biyu yayi kira a samar da wata doka da zata kauda kowane irin nau'i, na auren dole a tsakanin al’uma domin, kara kare, kima da mutuncin, auratayya da ma’aurata.

Sarkin, ya furta haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin shuwagabanin, kula da gyaran dokoki, ta jihar Kano, a fadansa, karkashen jagorancin, Justice, Wada Umar Rano.

Sarkin, na Kano, yace matakin ya zama wajibi, idan akayi, la’akari da yanda auren dole ya dauki sabon salon a wannan zamani.

Sarkin, yace yanzu wasu mutane, ne ke amfani da dukiya, ko mukami ko kuma wani abun hannun su, wajen jan hakalin makwadaitan, iyaye, domin aurar masu da ‘ya’ya.

Your browser doesn’t support HTML5

Auren Dole - 3'04"