Shan Magani Ba Bisa Ka’ida Ba Yana Da Illa Ga Mata Masu Ciki

Wasu mata masu ciki

Likitoci dake kula da mata sun yi gargadi da cewa, shan magani ba tare da izinin likita ba yana da hadarin gaske ga mata masu ciki.
Likitoci dake kula da mata sun yi gargadi da cewa, shan magani ba tare da izinin likita ba yana da hadarin gaske ga mata masu ciki.

Bisa ga cewar likitoci, shan magani ba bisa ka’ida ba yana iya sa mata masu ciki su yi bari ko kuma su kamu da wadansu cututuka da zasu iya zama da illa ga jaririn dake cikinsu, ko kuma su sa a haifi jariran da nakasa.

Bisa ga cewar likitoci, sabili da yanayin mata masu ciki, sau da dama wani abu dabam yake sa suji ciwon kai ko wani ciwon jiki dabam saboda ciki da suke da shi, saboda haka ya zama da muhimmanci su nemi ganin likita a maimakon zuwa su sayi magani a kemis.

Kwararru sun bayyana cewa, magunguna da ake sha domin kara samun koshin lafiya da gina jiki wadanda ake saya a kemis ba tare da bukatar izinin likita ba, yana iya zama da hadari ga mata masu ciki.

Likitoci sun kuma gargadi mata masu ciki kada su rika shan magungunan gargajiya domin gudun shan wani abu da zaama da illa gare su da kuma jarirai da suke dauke da su.