Majalisar jihar Neja ta gudanar da wani taro na jin ra’ayoyin Jama’a, dagane da kwaskwarima da akeso yiwa kundin tsarin mulkin Najeriya.
Majalisar, jihar ta Neja, tace zata tura ra’ayoyin jama’ar, jihar ga majalisar wakilai ta kasa kamar yanda aka bukace ta tayi.
Daga cikin mahimman batutuwa dai ake son tabowa a cikin kundin tsarin mulkin Najeriyar, har da batun baiwa majalisun, kananan hukumomin kasar yancin cin gashin kansu.
Shugaban marasa rinjaye, na majalisar jihar Neja, Hon. Nuradeen Umar, yace dama sun fara karbar takadun koke, daga wasu kungiyoyi dagane da batun kananan hukumomin
Wannan alamari na batun baiwa kananan hukumomi yancin daga jihohi, dai abune da ya dade yana daukar hakali matuka.
Your browser doesn’t support HTML5
Majalisar Jihar Neja