Shugaba Muhammadu Buhari A Wurin Taron Kolin Kasashe MAsu Arzikin Man Gas A Iran

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya, da shugaba Hassan Rouhani na Iran, da shugaba Vladimir Putin na Rasha da sauran shugabannin kasashe masu arzikin man gas a lokacin taron kolin da suka bude yau litinin a Teheran, babban birnin kasar Iran.
 

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya yana gaisawa da shugaba Hassan Rouhani na kasar Iran a lokacin da ya isa zauren taron kolin a Teheran.

Shugabannin da suka hallara a wurin taron kolin su na gaisawa da junansu

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya yana shiga dakin taron bayan ya gaisa da shugaba Hassan Rouhani na kasar Iran.

Shugabanni  acikin zauren taron kolin

Shugaba Hassan Rouhani, a dama, yana gaisawa da shugaba Teodoro Obiang Nguema Mbasogo na kasar Equatorial Guinea kafin a shiga zauren taro.