Shugaban Real Betis Ya Sauka - 3/29/14

Dan wasan Real Madrid, dana Real Betis na karawa a wasannin La Liga.

Kungiyar kwallon kafa ta Real Betis ta bada sanarwar cewa shugabanta Miguel Guillen ya sauka daga matsayinsa na shugaban kungiyar dake fama da wahalhalu, kuma za’a zabi sabon shugaba nan bada jimawa ba.

Guillen ya bada sanarwar ajje aikinsa ne a taron masu fada-a-ji na kungiyar da ake gudanarwa duk asabar, kuma Betis din tace za’a bayanna sabon shugaban a sa’o’i masu zuwa.

Betis dai yanzu itace kashin baya a laliga.