Siyasar 'Dalibai A Jami'o'i

Harkar siyasar matasa a Jami’o’i wanda ake kafa kungiya domin kwatowa matasa ko dalibai hakkokinsu, bincike dai ya nuna cewa a yanzu harkar siyasar dalibai ya sauya inda suke shiga harkar siyasar kasa, dangane da wanna batune wakiliyar dandalin VOA Baraka Bashir, ta zanta da shugaban kungiyar dalibai ‘yan asalin jihar Kano Usman Sani Shu’aibu mai dala.

Usman Sani Shu’aibu shugaban dalibai ‘yan asalin Kano dai ya bayyana yadda kungiyar dalibai take kokari wajen ganin cewa an baiwa ‘dalibai hakinsu, ya kuma kara bayani kan irin da dalibai ke takawa wajen ganin gwamnati ta kula da baiwa dalibai dama da biya musu kudin makaranta.

Saurari hirar don samun cikakken bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Siyasar Daliban Jami'oi - 3'31"