Tattaunawar Shugaba Jonathan da Manema Labarai

Shugaba Jonathan tare da 'yan jarida suna tattaunawa.

A jiya ne dai shugaban kasar Najeriya ya tattauna da manema labarai akan batutuwa dayawa, kuma manyan abubuwa biyu da akayi tattaunawar aka sune kan zabe da kuma batun tsaron kasa.

Da farko dai shugaban ya fara magana dai da sukar yadda mutane ke daukar yadda aka jirkinta zabe a kasa, yana fadin cewa a wasu jahohi za’a ga kashi talatin da biyar cikin dari na wadanda suka cancanci jefa kuri’a ne kawai suka sami katunansu na zabe, saboda haka idan anyi zabe kashi sittin da wani abu cikin dari na wadannan mutane bazasu iya jefa kuri’ar su ba koda kuwa suna so.

To amma wanan batu ya sake juyawa ya karkato kan babban batun rade radin da akeyi, na cewar akwai wani yunkuri da gwamnatin tarayya da PDP keyi na ganin cewar an cire shugaban hukumar zabe Farfesa Attahiru Jega, daga matsayinsa na shugaban hukumar zabe ta Najeriya, shugaba Jonathan, ya fara da fadin cewar dama ace Jega yana gurin sai manema labarai su fara tambayarsa, yakuma ce shine ya nada Jega da kwamishinonin zabe na jihohi dana tarayya na hukamar zaben, ya kuma kara da cewa a matsayinsa na wanda ya nada su kan kujerinsu idan har yaga kasawa ko wata gazawa cikin ayyukan da suke gudanarwa yana da ikon da zai ciresu.

Shugaba Goodluck Jonathan dai bai bada wata kwakwkwarar amsa ba kan tambayar da aka yi masa na cewar ko zai cire shi shugaban hukumar zabe Farfesa Attahiru Jega, ko bazai cire shi ba.