Wasu Matasa Sun Bankado Wata Almundahana Kuri'u

Matasa

An yaba da yadda matasan Karamar Hukumar Khana ta jihar Rivers su ka bankado wani yinkuri na wasu baragurbin jami’an Hukumar Zabe ta INEC, wadanda ‘yan kwanaki bayan kammala zabukan Shugaban Kasa da na Majalisun Dattawa da Wakilai, su ka buya suna dangwale-dangwalen yatsu kan takardun kada kuri’a (wato ballot papers), don jimlar takardun ta zo daidai da jimlar bogi mai bada nasara ga PDP da aka gabatar ma Hukumar Zabe, saboda sun ji kishin-kishin din yiwuwar zuwa Kotu.

Da ya ke yaba ma matasan, Shugaban Kungiyar Rajin Tabbatar da Adalci ta Network For Justice, Malam Aminu Sule, yace wadannan samari sunyi abun a jinjina musu kwarai da gaske don wannan babbar rawar gani ce, ganin yadda sukayi wannan bankade bankaden batare da tada wata hayaniya ba, ya kuma kamata a bama wadannan matasan lambar yabo don wannan wani abu ne da yakamata ace kowane dan Najeriya yayi ganin cewar hukumar zabe me zaman kanta INEC na kokarin kawo gyara a tsarin zabe a kasar baki daya.