Yadda Tsarin Hawan Nassarawa Yake Bisa Al'ada

Hawan Nassarawa, Kano

A shirin mu na Nishadi, wakiliyar VOA Hausa ta halarci Hawan Nassarawa a jihar Kano, domin ganin yadda ake shagulgulan babar sallah.

A bisa al’ada rana ta ukku bayan Sallar Eid ce ake Hawan Nassarawa, inda Sarkin Kano ke zagayawa unguwannin birnin Kano, ya je gidan Sarkin Nassarawa, sannan ya garzaya gidan gwamnati domin mika gaisuwar Sallah wa gwamna.

Kamar yadda yake a al’ada, akan taru akan titin gidan gwamna domin gaisawa da Sarki da tawagarsa, idan sun zo wucewa.

Wakiliyar Muryar Amurka Baraka Bashir ta samu yin magana da wasu daga cikin masu hawan, inda suka bayyana yadda hawan Nassarawa ke kasancewa.

Sun kuma zanta da Alhaji Idris Muhammad Sanusi wanda yake daga cikin 'yan rakiyar mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sunusi na Biyu. Alhaji Sunusi wanda aka fi sani da Babba Idi, ya bayyana yadda tsarin hawan Nassarawa yake bisa al’ada. A cewarsa hawan Nassarawa ya fi kowanne hawa janyo taron jama'a.

Ga cikakken rahoton daga wakiliyar DandalinVOA, Baraka Bashir.

Your browser doesn’t support HTML5

Yadda Tsarin Hawan Nassarawa Yake Bisa Al'ada