Yadda Yajin Aikin Malamai A Shekarar 2022 A Najeriya Ya Nuna Girman Matsalolin Ilmi A Kasar
Your browser doesn’t support HTML5
Da zarar aka yi batun harkar ilimi a Najeriya a shekarar 2022, babban abin da ke zuwa ran mutane da dama shi ne yajin aikin sama da wata takwas da malaman jami’o’i suka yi. Yajin aikin dai ya nuna irin girman matsalolin da ake fama da su a bangaren ilimi a Najeriyar.