'Yan Kungiyar Kato Da Gora Sunce A Shirye Suke

Maharba da Kayan Yakinsu.

Samari ‘yan sa kai 'yan kungiyar ‘yan kato da gora da aka fisani da suna sibiliyan JTF sunyi wani atisaye don kara azama da kuma bama sojojin Najeriya gudun mawa don yakar ‘yan kungiyar Boko Haram. A cewar shugaban hadakar kungiyar maharba ta jahar Adamawa Alh. Mohammadu Usman Tula yayi Karin bayani kan cewar a shirye suke su fuskanci duk wata, wuta da zata fito daga bangaren ‘yan kungiyar ta Boko Haram, basu tsoron komai, su dai bukatar su shine al’umma su cigaba da sasu cikin addu’a don neman nasara da ga wajen Allah baki daya.

Shi kuma Alh. Adamu Garbajo wani kusa a jam’iyar hamayya ta APC yace yakamata gwamnati da dubi yada yakamata don ta taimakama wadannan matasan ganin cewar bas u da albashi don suna rawar gani kwarai da gaske.

Bugu da kari jama’ar garuruwan da aka kwato daga hannun yan kungiyar Boko Haram na ta farinciki da wannan nasarar da ‘yan kungiyar kato da gora su ka samo.

Your browser doesn’t support HTML5

Yan kato da Gora