'Yan sanda Na Kewaye Da 'Yan Bindiga A Nairobi

Mutane na gudu daga Westgate Mall lokacin da 'yan bindiga suka bude wuta a wurin

Hukumomin kasar Kenya na ci gaba da kokarin neman kama maharan da ke boye a cikin Westgate Mall
Har ya zuwa jijjifin lahadin nan hukumomin kasar Kenya a birnin Nairobi, na ci gaba da aiki wurjanjan su na kokarin kama 'yan bindigar da suka kashe mutane 39 tare da raunata wasu fiye 150 a cikin wani mummunan harin da aka kai wata cibiyar hada-hadar ksuwanci mai tulin kantuna daban-daban. Hukumomin sun ce jami'an tsaro sun yiwa maharan kawanya a inda suka buya tun jiya asabar a cibiyar kasuwancin ta birnin Nairobi da ake kira Westgae Mall, kuma an yi amanna cewa maharan sun kama mutane su na yin garkuwa da su. Kungiyar 'yan ta'addan kasar Somaliya ta al-Shabab ta dauki alhakin kai harin.

Wakilin Muryar Amurka a Nairobi babban birnin kasar Kenya ya ce akwai damuwar cewa watakila wasu daga cikin maharan sun tsere bayan harin.

Jim kadan bayan harin shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta yayi wani jawabin neman kwantar da hankulan 'yan kasar ta Kenya wadan harin ya kidima. Shugaban kasar yayi tir da harin wanda ya ce aiki ne na matsorata sannan ya jinjinawa 'yan kasar ta Kenya saboda yadda suka nuna hadin kai cikin barazanar ta ta'addanci.Shugaba Kenyatta ya lashi takobin cewa za a kama wadanda suka yi wannan ta'annati kuma za a dauki mataki a kan su. Ya ce gwamnati a shirye ta ke ta kare kasar cikin ta da wajen ta.

Shugaban kasar Kenya uhuru Kenyatta



'Yan bindigan sun bude wuta da bindigogi tare da jefa gurneti a cibiyar hada-hadar kasuwancin ta Westgate Mall a lokacin da jama'a ke tsakar sayayya. Har da yara a cikin wadanda suka ji ciwo. Canada da Faransa sun ce ana kashe musu mutane bibbiyu a cikin harin, Amurka ta ce babu Amurkawa a cikin wadanda suka mutu, amma an samu wadanda suka ji ciwo.