Kafar sadarwar radiyo taci gaba da zama mai tasirin gaske a birane da karkara, inda jama’a kan saurari radiyo a lokacin da suke tukin mota dama lokacin da suke hutawa.
Hakanan a kasashen da ba wadatar wutar lantarki, mutane kan dogara ne ga radiyon don samun labarai har ma a gandun daji. Wannan rana da Majalisar Dinkin Duniya, ta ware don radiyo ta samo asaline daga fara sadarwar Majilasar Dinkin Duniyar, a alif dari tara da arba’in da shida.
Majalisar Dinkin Duniya dai zatayi bikin murna birnin Janiba, a ayau Juma’a. A kwai kuma bayani daga sakataren majalisar Banki Moon, don murnar cikar kungiyar sadarwar duniya shekara dari da hamsin da kafuwa.