Yiwuwar Yin Zabe Ga ‘Yan Gudun Hijiran Najeriya.

'Yan gudun hijira sandiyar hare-haren 'yan Boko Haram sun karban kayayyakin agaji da suka hada da abinci a sansanin 'yan gudun hijira a Yola.

Shugaban hukumar zaben Najeriya Attahiru Jega, ya fadi cewa babu yadda za a yi a juya fasali ko yin jabun katin zabe na din-din-din, a taron tabbatar wa ‘yan gudun hijira damar kada kuri’a a zabe mai zuwa na watan gobe da za’ayi.

Jega ya kara da cewa aikin banza ne in har wani ya sayi katin zabe, don muddin ba wanda aka yi ma rijistar bane ya bayyana a rumfar zaben, na’ura ba zata amince ba.

Hukumar ‘yan gudun hijirar Najeriya dai tace akwai sama da ‘yan gudun hijira dubu bakwai a sansanoni dabam-dabam a fadin kasar bayan ga dinbin ‘yan gudun hijirar dake fake a gidajen dangi da wadanda ma ba a san inda suke ba.

Saurari rahotan Nasiru Adamu.

Your browser doesn’t support HTML5

Taron Tabbatar wa Da 'Yan Gudun Hijira Kada Kuri'unsu - 3'53"