Za'a Buga Wasan Sada Zumunta Tsakanin Jamus da Spain Batare da Mai Tsaron Gidan Kasar Jamus ba

Mai tsaron gidan kasar Jamus,Manuel Neuer

Mai tsaron gidan kungiyar wasan kwallon kafar kasar jamus, Manuel Neuer, bazai sami buga wasan sada zumutar da za suyi da kasar Spain ba saboda ciwon da yaji a gwiwar sa.

Amma, Koch din kasar Jamus, Joachim Low, ya rage da zabi biyu, koya dauko, Roman Weidenfeller, na Borussia Dortmund, ko kowa Ron-Robert Zieler, na Hanover, domin, maye gurbin Manuel, a karawar da zasu yi ranar talata, mai zuwa da kasar Spain.

Koch din na Jamus, yace ko da yake yaso ya fuskancin Kasar ta Spain, da ‘yan wasan mafiya kyau, ba zai yi kasadar amfani da Manuel ba saboda ciwon sa.

Amma ya kara da cewa ko da yake Manuel, ba zai samu buga wasan ba, akwai wadanda zasu iya maye gurbinsa wandada suma abun dogaro ne.

Your browser doesn’t support HTML5

Jamus da Spain - 1'00"