Zama Kusa Da Dam Na Hadassa Kamuwa Da Malaria

Ana yada kwayoyin cutar Malaria ta macen sauro kamar wan nan da aka gani awan nan hoto.

Sakamakon wani sabon bincike da aka gudanar, ya nuna cewa, mutanen da ke zaune a kusa da madatsun ruwa na fuskantar barazanar saurin kamuwa da cutar zazzabin cizon sauro sau hudu fiye da wadannan ba sa zaune a kusa da dam din a kasashen da ke Kudu da Hamada a Afrika.

Binciken har ila yau ya nuna cewa, yayin da ake shirin gina madatsun ruwa da dama a yankin, za a samu karin dubun dubatar masu kamuwa da cutar a wannan shekara.

Sakamakon binciken da aka wallafa a wata mujalla mai suna “Malaria Journal” a turance, ya yi nazari ne kan inda aka gina wadansu madatsun ruwa dubu 1,270, wadanda ya alakanta da matsalar zazzabin cizon sauro.

Ya kuma gano cewa fiye da mutane miliyan daya a kasashen Kudu da Hamada, za su kamu da cutar Malaria a wannan shekara saboda suna zaune a kusa da wadannan madatsun ruwa.

Mathew McCartney, na cibiyar da ke kula da yadda ake sarrafa ruwa a kasashen duniya, shi ne ya jagoranci wannan binciken da ya yi dubi kan wadansu madatsun ruwa 78 da ake shirin ginawa a wadansu kasashen Afrika.

Bisa ga binciken, idan aka kammala gine-ginen, za a samu karin wadanda za su kamu da cutar zazzabin cizon sauro, wadanda adadinsu zai iya karuwa zuwa dubu 56 a duk shekara. Binciken ya kuma bayyana matakan da za a iya dauka domin kare samun karin mutanen da za su kamu da zazzabin cizon sauron, kamar yadda McCartney ya bayyana.

Ga Sarfilu Hashim Gumel da fassarar rahoton wakilin Muryar Amurka Joe De Capua.

Your browser doesn’t support HTML5

Bincike kan zazzabin cizon sauro-3"