Dan takarar jam’iyar APC, Bola Tinubu ya lashe zaben shugaban kasa bayan ya sami kashi 36% na kuri’un da aka kada a zaben shugaban kasa da aka gudanar ranar asabar, yayinda dan takarar jam’iyar PDP Atiku Abubakar ya zo na biyu da kashi 30% dan takarar Jam'iyar Labour Peter Obi kuma ya zo na uku da kashi.26%.
Tinubu ya doke sauran ‘yan takara goma sha takwas da kuri’u APC-8,794,726, yayinda dan takarar jam’iyar PDP Atiku Abubakar ya sami kuri’u 6,984,520, Peter Obi na jam’iyar Labour ya sami kuri’u 6,101,533, yayinda dan takarar jam’iyar NNPP-Rabi’u Musa Kwankwaso 1,496,687.