Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tarayyar Turai Zata Ba Najeriya Euro Miliyan 55 Don Yakar Polio


Wani magidanci ya kawo dansa cikin kwale-kwale ana diga masa maganin rigakafin Polio a yankin Niger-Delta na Najeriya

An zabi jihohi 24 da zasu ci moriyar wannan tallafin da ya hada har da na gudanar da sauran ayyukan rigakafin cututtuka dabam-dabam

Kungiyar Tarayyar Turai ta kebe Euro miliyan 55 (Kimanin Naira Miliyan Dubu 11) domin yakar cutar Polio da kuma gudanar da ayyukan rigakafin wasu cututtukan masu yin kisa a jihohi 24 na Najeriya.

Manaja mai kula da ayyukan tallafawa rigakafi a Najeriya na Majalisar Tarayyar Turai, Dr. Ayeke Anthony, yace Tarayyar Turai ta kuduri aniyar tallafawa Najeriya wajen rage mace-macen jarirai da yara kanana, da kuma kawar da kwayar cutar nan dake haddasa shan inna, WPV, daga kasar.

Yace an zabi jihohi 24 domin gudanar da wannan aikin, kuma an kasa shi gida biyu. Kashin farko zai ta'allaka ne ga yaki da cutar Polio ko shan inna.

Jihohin da zasu ci moriyar wannan kashin farko sune Gombe, Kebbi, Plateau, Lagos, Ogun, Abia, Akwa-bom, Edo, Cross River.Kashi na biyu kuma zai lashe Euro miliyan 35, sannan za a gudanar da shi ta hannun Hukumar Kiwon Lafiya tun Daga Tushe ta Kasa a jihohi 24 da aka zaba
XS
SM
MD
LG