Jami'an ma'aikatar tsaron kasar Aljeriya sun ce wani bom da ya fashe a yammacin kasar ya hallaka jami'an tsaro bakwai, da suka hada da sojoji uku, da 'yan sanda hudu. Sun mutu ne gaba dayan su a jiya asabar lokacin da wani bom da aka turbude a gefen hanya yayi bindiga a garin Sidi Chaib, ma kimanin tazarar kilomita 440, yamma da Algiers ko Alger, babban birnin kasar.
A cikin wata sanarwar da ta gabatar a shafin ta na bayanai a intanet, ma'aikatar tsaron kasar Aljeriya ta ce harin bom din ya rutsa da sojojin ne a lokacin da suka kaiwa jami'an tsaron garin dauki.
Ma'aikatar tsaron ta kara da cewa :" irin wannan mugun aiki na masu aikata babban laifi, ba abun da yake yi, illa karawa sojojin kasar kaimi da kwazon ci gaba da kakkabe wadannan kugiyoyin 'yan ta'adda, kuma su raba kasar da munanan ayyukan su na keta.