Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabar Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce ana Bukatar Karin Kwararrun Ma'aikatan Kula da Lafiya a Yammacin Afirka

Ma'aikatan Cutar Ebola
Ma'aikatan Cutar Ebola

Shugabar Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce ana bukatar karin kwararrun ma'aikatan kula da lafiya a Yammacin Afirka domin a dakile karuwar barkewar cutar Ebola.

Da take magana a yau Jumma'a a wajen wani taron manema labarai a Geneva, Dr. Margaret Chan ta ce yawan wadanda cutar ta hallaka sun haura 2,400, kuma jimlar wadanda ke dauke da cutar ta kai 4,784.

Ta ce jami'an dake kokarin dakile yaduwar cutar na fama da karancin kusan komi, kama daga kayan rufe jiki na musamman, zuwa dakunan gwaje-gwaje na tafi da gidanka, da su jakankunan leda na daukan gawa. Amma ta ce abu mafi girma dake yin cikas shi ne rashin kwararrun ma'aikatan kula da lafiya.

Hukumar Lafiya ta Duniya ,WHO/OMS, ta ce a wannan mako cutar Ebola ta kashe ma'aikatan jinya kusan 80 a Laberiya, kasar da ta fi ganin arkane da shan bonen cutar.

Chan ta ce ana bukatar ma'aikatan jinya fiye da 1,000 a cibiyoyin yaki da Ebola da aka kakkafa a yankin. Ta yi lale marhabun da alkawarin da kasar Cuba ta yi a yau Jumma'a na cewa za ta turawa Yammacin Afirka kwararrun ma'aikatan kiwon lafiya 165. An shirya cewa a farkon watan gobe na oktoba za su je kasar Saliyo su yi watanni shida a can.

Cibiyar rigakafi da yaki da cututtuka ta Amurka, CDC ita ma ta tura ma'aikata su taimaka a yi yaki da barkewar cutar, ita ma hukumar raya kasashe masu tasowa ta Amurka, USAID ta na neman kwararrun likitocin da za ta tura yankin. Masu son taimakawa na iya mika takardun su na neman aiki a shafin ta na intanet a www.usaid.gov

Jami'an MDD da suka hada da babban magatakardan majalisar, Ban Ki-moon sun yi kashedin cewa ana bukatar wani kwakkwaran matakin dakile yaduwar Ebola, muguwar cutar dake sa haraswa, da gudawa, da zubar jini ta idanu da kunnuwa da duka sauran kafofin dake jikin mutum.

XS
SM
MD
LG