Drone, wani sabon mashin na kimiyya da aka kirkiro ne, don cinma abubuwa da dama, wasu mutane su kanyi amfani da shi wajen nishadi, wasu kuma su kanyi amfani da shi wajen kasuwanci, kamar masu fina-finai, su kanyi amfani da shi wajen daukar hoto a lokacin da suke wasan kwai-kwaiyo. Kana kuma akanyi amfani dashi wajen leken asirin kasa, koma a ce sojoji kanyi amfani da shi wajen kai hari ga abokan hamanyya.
A duk dai cikin kokarin ayi amfani da wannan mashin din, wajen ciyar da al’uma gaba, anyi mishi wani sabon tsari wanda zai dinga kai sako idan mutun ya siya abu ta yanar gizo. Ba zai jira sai wani mutun ya zo kofar gidan shi don kawo sako ba. Shi dai wannan mashin din, za’a dinga amfani da shi wajen isar da sako cikin gaggawa, wanda hakan kan iya samar da karin yawan rashin aikin yi. Tunda za’a dinga juya akalar wannan jirgin ne daga waje daya, shi kuwa yana can yana yawo cikin sararin samaniya, har sai ya kaiga masaukin shi.
Wasu kamfanonin sun shiga cikin wannan tattaunawar kamar su kamfani Google, da DHL, ana kuma sa ran fara amfani da shi nan ba da jimawa ba, a kasar Austrelia, da Germany, shi kuwa wani kamfani kasar Farance na horas da ma'aikatan da zasu ja akalar jirgin.