Abubuwa biyar da zasu taimaka ma mutun matuka, wajen samun damar yin bacci kamar jariri. Na farko, shine mutane su rungumi rana musamman ta hantsi, domin kwa-kwalwa na bukatar rana, bayan wayewar gari. Rana tana tai makama sinadaran da suke rike jiki, da basu abinci da sukan bukata bayan tashi daga bacci, da kuma tsara jikin mutun don baccin dare idan lokacin yayi.
Abu na biyu, motsa jiki shima wani abu ne mai matukar taimaka ma jiki, kuma da ba jiki kuzarin da zai bukata, haka kuma motsa jiki zai taimaka ma mutun yin bacci a dai-dai lokacin da ya kamata. Na uku, akwai bukatar muta ne su san wane irin abinci suke ciki, domin kuwa cin abinci masu gina jiki, suna tai makawa kwarai wajen samun lafiya mai inganci. Akwai bukatar mutune su yawaita cin, ‘yayan itatuwa, da kuma rage yawan cin abinci mai dauke da sinadarin “sitaci”. Kana hadari ne ga lafiya a kwanta bayan cin abinci.
Na hudu, akwai bukatar mutun yayi wanka a'kalla sau biyu a rana, da ruwa masu dumi idan yanayin zai bari, ayi amfani da sabulu da ke dauke da sinadaran gyaran jiki. Na biyar kuwa, akwai bukatar mutane su dinga daga kafafuwan su sama, domin yin hakan yana taimakama wasu jijiyoyi da jini yawo a wasu sassan jiki.