Mafi akasarin matasa musamman maza, basu da kokarin taimakon iyayen su a gida, da wasu aikace-aikace. Sau da dama za’a ga samari matasa, basu da tunanin yin wani aiki a gida don bama iyayen su taimako. Amma wannan laifine daga bangaren iyayen kokuwa?
Wata mata mai suna Alias Estella, ta rubuta a shafin ta na facebook, wata yar jejeniya da tayi da dan ta mai suna Aaron, dan shekaru goma sha uku 13, da cewar, idan har dan nata ba zai taimakama ta da wasu aikace-aikacen gida ba, to yasan da cewar baza ta daukar mishi wannan halinba.
Ta zayyana mishi sharadi da sai ya bisu kamin ya zauna a cikin gidan ta, idan ba haka ba kuwa zata cishi tarar kudi. Abu na farko shine, dole ya dinga gyara dakin shi a kowace safiya, dole ya wanke ban-dakin shi a karshen kowa ne sati, dole ya wanke kwannon da yaci abinci a koda yaushe. Idan kuma ya karya doka daya daga cikin wannan dokokin, zata cishi tarar dallar Amurka $30.
A karshe ta shawarci iyaye, da su dinga sa ma ‘yayan su dokoki a gida, wanda idan suka taka dokar sai a hukunta su. Ta ba ma matasa shawara da cewar, su dinga kokari wajen taimaka ma iyayen su da ayyuka da suke na gida, domin kuwa suma idan suka kai ga wannan matsayin zasu so ace ‘yayan su sun basu irin wannan taimakon.