Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shafufukan Yanar Gizo Na Taimakawa Matasa Wajen Zaben Jami'a

Shafufukan yanar gizo
Shafufukan yanar gizo

Zamanin kimiyya da fasaha ya zo da abubuwa da dama, wanda wasu na ganin akwai alfanu kuma akwai rashin shi ga wannan zamanin na “Technology” a turance. A wasu bincike da aka gudanar a wannan zamanin, akwai abubuwa da dama da suka saukaka yadda matasa ke gudanar da rayuwar su cikin sauki da cigaba.

Daukar hoton kai-da-kai wanda ake cema “Selfie” masana naganin shi a matsayin wani abu da ke da matsaloli da dama ga matasa, kama da ga rage karfin ido, a dai-dai lokacin da ake sa hasken wutar waya a lokacin da ake daukar hoto, domin kusancin ido da hasken. Sai yadda abun ke taba kwakwalwa, da abubuwa da dama makamantan haka.

Wani sabon salo da matasa musamman ‘yan-sakandire keyi yanzu shine, sukan zabi makarantar jami’a da suke son zuwa, ta duba wane mataki makarantar take a wajen saka hotunan dalibai, da na gine-ginen makarantar a shafin su na “Intagram” Yanzu haka dai matasa sukan duba suga mutane, nawa ke nuna sha’awar ta makaranta kamin su yi matsayar ko zasu je makarantar kokuwa. A takaice za’a iya cewar shafufukan yanar gizo na taimakawa, wajen dalibai su zabi irin makarantar da zasu je da irin abokai da zasu sama a makarantun ta duba shafufukan yanar gizon makarantar.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG