Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Cigaba Da Zargin Saurayi Gordon Da Kashe Budurwar Shi

Bobbi Kristina Brown
Bobbi Kristina Brown

Ana zargin matashin nan Nick Gordon, saurayin Bobbi Kristina Brown, da kashe ta da allurer guba da yayi mata. Ita dai Kristina, ‘yayyar tsohuwar mawakiyar nan ta kasar Amurka, ce wato Whitny Histon, haka kuma babanta shima tsohon mawaki ne da yayi tashe a shekarun baya wato Bobby Brown.

Ita dai yarinyar a kwanakin baya aka tsince ta a cikin bayi, ta fita cikin hankalin ta, bayan kaita asibiti da ‘yan kwanaki ta mutu. Rahotannin na cewar yarinyar ta mutu ne a Otel din da maihai fiyar ta, ta mutu kuma a irin yanayin da mahaifiyar ta, ta mutu itama. Amma ana ganin kamar shaye-shayen hodar ibilis ne tayi sanadiyar mutuwar ta kamar ta mahaifiyar ta.

Kamar yadda wani shafin Tsegumi ya ruwaito, wata kungiya mai suna “conservator Bedelia Hargrove” suka kai karar saurayin yarinyar Gordon a watan Yuni, suna zargin shi da take hakkin yarinyar Brown, sa'o'i kafin ta da aka samu fuskar ta cikin wani kwanon wanka a ciki otel.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG