WASHINGTON DC, —
A jihar New Delhi, ta kasar Indiya, wani gidan “Zoo” wato inda ake ajiye dabbobin daji, an kai wani Damisa mai shekaru goma sha biyu 12, wanda aka yi kokarin hada shi da wata Damisa macce, don ganin ko zasuyi sabo da juna. A tabakin jami’an gidan Zoo din jiya Asabar, an dai maida damisan inda aka dauko shi, bayan tsawon wata biyu, daga yankin kudancin kasar a jihar Kerala.
Ana dai yima damisar lakabi da suna “Salman” dama an aro shi daga wani gidan zoo a kudancin jihar Kerala a karshe watan Augusta, amma rashin nuna sha’awar shi ga wata damisa yasa masana na gani cewar yayi girma da yawa, a tabakin ma’aikacin gidan zoo din Mr. Riaz Khan, ya shaida wa manema labarai cewar, maccen damisar tayi kokarin yaudara namijin, amma shidai ya nuna kasalar shi a fili.
Amma abun da suka lura shine, shi damisan namiji ya fahimci cewar, ita damisar macce, ba jinsin su daya ba don haka yasa bashi da sha’awar kusantar ta. Domin kuwa a yankin kasashen Asiya, suna da jinsin damisoshi da dama, amma idan ba mutun yasan ban-bancin suba, ba zai iya ganewa ba, zai dauka duk iri daya ne.
Ita dai damisa da ake kira “Jaguars” tana kama da damisa, ammabambanci kasancewa suna da ratsin baki a cikin su. Damisa kuwa tana da guntu kafafu da kuma wutsiya.