Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tausayi Bangare Ne Na Hallita A Rayuwar Dan'Adam Da Dabbobi

giwar ruwa
giwar ruwa

Sau da yawa mutane kanyi tunanin dabbobi basu da hankali ko basu da tausayi. Wani abun mamaki da ya faru da wata jaririyar dabbar ruwa, da ake kira “Seal” a turance, wato giwa ruwa. Ita dai jaririyar giwa ruwa, ta makale a cikin tabo, kuma bata samu wanda zai tai makamata ba.

Ta kwashe tsawon lokaci, wanda har tana neman rasa ran ta, ana cikin haka sai ga wasu ayarin tawagar shanaye, su kayi da’ira akan wannan dabbar, hakan dai ya jawo hankalin masu kula da wannan gidan dabbobin. A cewar mai tsaron wajen, a lokacin da ya lura shanayen sun tsaya a wajen, wanda ya sabama al’adar ta tsayawan su a wajen ya jawo hankalin shi.

Domin kuwa shanaye basu tsayawa a wajen, hakan yasa ya tashi don fahimtar menen dalilin daya sa sukayi da’ira a wajen. Isar shi ke da wuya sai ya lura da cewar wannan jaririyar giwar ruwace ta makale, suna tausayin ta. Hakan yasa aka kaima giwa ruwar dauki. Bayan dauke dabbar shanayen ba suyi wata-wata ba sai suka cigaba da tafiyar su inda suka nufa. Haka ya nuna cewar suma suna da tausayi.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG