Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bayan Shekaru 10,000 Jikin Wasu Zakuna Basu Canza Ba

Zaki
Zaki

Taron manazarta a wani gari “Permafrost” na yankin arewa maso gabashin kasar Siberia, sunyi ittifakin cewar, wasu gangar jikin zakuna guda biyu da aka gano a wani kogo, sun kai tsawon yawan shekaru kimanin dubu goma 10,000. A cewar su wannan wani babban abun al’ajabi ne, domin kuwa jikin nasu bai canza ba daga yadda yanayin zaki yake.

Suna dai tsammanin cewar wadannan, zakunan sun fito farauta ne, wanda suka biyo Gada, dalili kuwa shine sun tarar da hakoran zaku nan a dai-dai wajen suma basu yi komai ba. Dama dai a wannan yankin akan samu abubuwan ban'al'ajabi a kusan kowane lokaci, sai dai wannan shine yafi kowannen abun mamaki da al’ajabi.

Masanan dai sunyi nuni da cewar, hakan ba zai zama abun mamaki ba, saboda irin yanayi da ake da shi a kasar ta Siberia, komai kan iya zama har fiye da hakan. Ana sa ran dai za’a cigaba da gudanar da bincike a kan wadannan abubuwan mamakin, wanda a watan gobe za’a fitar da rahoto a hukumance.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG