Yana daga cikin abubuwa da sukan sa mutane su dinga gudun mutun, idan mutun ya cika tambaya, kuma ya kasance baya bayyanar da irin na shi labarin ga mutane. Shi dai kawai yana so yaji labarin mutane amma yana boye na shi labarin. Da yawa mutane basu samun natsuwa da irin wadannan mutane.
Haka kuma duk mutun da yake yawaita saka hoto wanda yayi kusanci da yawa, kamar hoton fuska babu sauran guri da zai bayyanar da sauran jikin mutun, ko wajen da mutun yake. Shima wannan yanasa mutane su dingan yima mutun wani kallo. Masu binciken sun kara da cewar duk mutun da ya kasance baya kokarin gyaran jikin shi, wanda zai shiga jama'a amma yana wani wari, shima mutane basu cika son ganin shi kusa da su.
Haka kuma idan mutun ya zamana baya bayyanar da damuwar shi ga mutane, don sun taimaka mishi, shi ma yana iya fuskantar rashin jituwa a tsakanin shi da mutane. Ko aga mutun ya cika kirki. Wato mutun ya zama shi ko da yaushe yanaso musamman abokan shi. Haka kuma mutun ya dinga wasu abubuwa, don ace yanada kirki ko yana da hakuri. Hakan zai nuna cewar mutun ba da gaske yake ba, abun da yafi kamata da mutun shine ya nuna gaskiyar halayen shi a cikin jama’a a kowa ne irin hali ya samu kanshi.