Abubuwan mamaki basu taba karewa a fadin duniya, idan kuwa kaji ance sun kare to labarin mutun ne yazo karshe. Mafi akasari a fadin duniya, anfi sanin Mage “Kyanwa” da Kare, a matsayin abubuwa da mutane kan ajiye a matsayin dabbobin gida. Hasali ma akan koya musu wasu dabi’u da sukan ba mutane nishadi a lokutta da dama.
Amma abun mamaki sai ga wasu mutane a wasu kasashe daban daban sun dauki wasu dabbobin daji a matsayin dabbobin ajiya a gida. Wani manomi mai suna Zhang Xianping, mazauni garin Zhangjiakou a kasar China, yana da wani Alade da yakai girman dan-maraki. Kuma yana hawan shi zuwa wurare da yawa.
Shima wani mai wasan gwaninta na dusar kankara yana da Agwa-gwa a matsayin dabbar shi abun so, wanda yake mata kwalliya kamar wata jaririya, dan kasar China. Ita ma Zhu Roumeng, mazauniyar kasar China, tana da Alade, kuma takan kwanta dashi a kan gado suyi ta cudedeniya da shi, harma sukan fita yawo tare. Tana mishi abubuwa kamar yadda zatayi ma dan-mutun.