Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fittacciyar Mawakiya "Selena Gomez" Ta Fada Kwata

Ana iya cewa wannan shekarar dake neman karewa, tazo da wasu abubuwan al’ajabi ke nan a duniyar fitattun mawaka da ‘yan fina-finan “Holly Wood” ke nan? Shahararriyar yarinyar nan da ta fara wasan yara tun tana ‘yar karamar ta, wadda daga baya ta fara wakoki, wato “Selena Gomez” Kana kuma tsohuwar budurwar fitaccen matashin mawaka wato "Justine Bieber"

Ta saka katafaren gidan ta a kasuwa, a shekarar da ta gabata ne, ta siya wannan gidan wanda yake kusa da babban birnin Los Angeles, gidan dai na da dakuna biyar 5, da bayi shida 6, kana da wajen motsa jiki, sai wani gini a gefe, wannan katafaren gidan dama yafi karfin ace yarinya mai shekaru ashirin da uku 23, ke cikin shi.

Daki daya kawai na gidan yafi girman wani gida, tana dai neman mai saye akan kudi dallar Amurka $4.5M milliyan hudu da dubu dari biyar. Wanda yayi dai-dai da naira milliyan dubu dari tara da casa’in 990,000,000. Idan ba’a manta ba a ‘yan kwanakin baya ne rahotannin suka ruwai to wani sannane dan wasan boxin ya fitar da gidan shi yana neman mai saye.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG