Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Cafke Wani Mai Sayarda Yara

An gurfanar da wani manomi mai shekaru 49. Mai suna Gabriel Ajor, a gaban kotun a Lokoja a jihar Kogi ana tuhumarsa da laifin sace yara bakwai da kuma sayarda su a ciki har da ‘ya’yan cikin su biyu masu shekaru takwas da shekaru biyu .

Shi dai Ajor, ya dauki yaran ne da niyyar cewa zai kai su karatu a Owerri da kuma kasar Amurka akan kudi Naira dubu dari hudu.

Jaridar Vanguard, ta ruwaito cewa Ajor, ya yaudari iyayen sauran yaran biyar ne Kenneth Omale da John Attah, ne cewa hakikatan zai tuira ‘ya’yansu zuwa makaranta.

Dan Sanda mai gabatar da kara ASP, Cornet Ayabatu, ya ce wanda ake tuhumar sun hada bakin da wasu abokan sa wadanda ake nema a yanzu haka su aikata wannan laifin.

Yaran masu suna Goodway Kenneth, shekaru 5, Kindness Kenneth, shakaru 3,Shedrack John, shekaru 6, Goodday John,6, da Confidence Ojonuba, 8 dan watani takwas.

Sauran sun hada da Gift Gabriel shekaru 6, da Destiny Gabriel shekaru 3, an ce duk ‘ya’ya masa daga cikin yaran an kaisu wanni wuri na daban.

Ayabatu Ajor, ya amsa cewa wani mutun mai suna Malik, a Owerri ya biya shi Naira dubu dari hudu ne akan yaran bakwas.

XS
SM
MD
LG