Kungiyar kwallon kafa ta Besiktas ta yi kunnen doki 1-1 da Napoli
Manchester City ta lallasa takwaranta ta Barcelona daci 3-1
Atletico Madrid ta samu nasara akan Rostov daci 2-1
Luda Razgd tasha kashi a Arsenal daci 3-2
PSV nada 1 Bayern Munich na da 2
Itama Kungiyar Basel bata ji da dadiba a hanun PSG daci 2-1 a gidanta
Borussia Monchenglabach ta yi canjaras 1-1 tsakaninta da Celtic
Benfica ta sha Dynamon Keiv 1-0
A yau kuma za'a cigaba da sauran wasannin rukunin inda kungiyar kwallon kafa ta Legia Warsaw zata kara da Real Madrid
Sevilla zata karbi bakuncin Dinamo Zagreb
Borussia Dortmund kuwa zata fafata ne da Spoting CP
Juventus zata kece raini da Lyon
Kobenhange da Leicester City
Ita kuwa Tottenham zata kara ne da Bayern Leverkusesn
Monaco da CSKA Moscow
Porto ta karbi bakuncin Club Brugge
Za'a kece raini da misalin karfe tara saura kwata na dare agogon Nejeriya da Nijar da kuma kamaru.
-
Bala Branco
Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.
-
Ibrahim Jarmai
Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.