Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rakiya Abubakar Daya daga cikin 'Yan Matan Chibok da Aka Cetota da Wasu 'Yan Boko Haram da Suka Mika Kansu

Jiya sojojin Najeriya suka ceto Rakiya Abubakar daya daga cikin 'yan matan Chibok da Boko Haram ta sace tun shekarar 2014 tare da danta mai watanni shida.

Kafin sojoji su kubuto Rakiya sun nunawa manema labarai wasu mutane goma 'yan Boko Haram da suka ce su suka mika kansu da kansu tare da makamansu suka kuma yi nadama.

Mutanen sun nemi gafara a wurin Najeriya da jama'arta suna cewa abubuwan da suka yi ba masu kyau ba ne. Sun kira 'yanuwansu dake daji su fito su tuba domin ba za'a kashesu ba. Zasu samu masalaha kamar yadda suka samu.

XS
SM
MD
LG