Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yanmajalisar dokokin Somalia sunyi zargin cewa makwapciyarsu, kasar Habasha (Ethiopia) na nan tana bi ta bayan gida...


‘Yanmajalisar dokokin Somalia sunyi zargin cewa makwapciyarsu, kasar Habasha (Ethiopia) na nan tana bi ta bayan gida, tana aikawa ‘yan tada zane-tsayen Somalia makamai don su rinka tada wutar rikici a cikinta.

A jiya ne wadanan ‘yan majalisar na Somalis suke wannan zargin a birnin Nairobin Kenya, inda har yanzu nan ne mazaunin gwamnatin wucingadin da aka kafawa Somalia – kasar da, rabonta da gwamnati an fi shekaru 14.

Daya daga cikin ‘yanmajalisar na Somalia, Abdallah Haji Ali, yace shi da sauran ‘yanmajalisar tasu duk sun damu da yiyuwar barkewar kazamin tashin hankali a lardunan Bakool da Bay dake tsakiyar Somalia din. Yace kuma in ba domin taimakon da Ethiopia ta dade tana baiwa ‘yantawayen ba, da tarzomar bata kawo yanzu ana yinta ba.

XS
SM
MD
LG