Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Condoleezza Rice ta roki musulumin duniya


Sakatariyar Harakokin wajen Amurka Condoleezza Rice ta roki Musulmin duniya da su yi ma Allah su yi watsi da kiraye-kirayen yin tashin hankali daga mutanen da su ka kufula saboda rahotannin da kafofin yada labarai su ka bada game da zargin cewa Amurkawan da ke yin tambayoyi ga mutanen da aka kama, sun wulakanta Al-kura’ani mai tsarki.

Ms.Rice ta ce Amurka ba za ta taka yarda da rashin girmama Al-kura’ani ba. Ta ce ana gudanar da cikakken bincike game da zargin wulakanta Al-kura’ani a gidan kason Guantanamo, sannan ta ce, idan zargin ya tabbata, Amurka za ta dauki matakin da ya dace.

Ta gabatar da wannan sanarwar ce a daidai lokacin da zanga-zangar nuna kyamar Amurka a biranen Afghanistan da dama, su ka yi sanadiyar mutuwar wasu mutane ukku kuma a jiya alhamis. Ma’aikatar tsaron Amurka ta ce har ya zuwa wannan lokaci ba’a samu wata shaidar da ke tabbatar da ikirarin ba, bayan wani binciken da aka gudanar game da zargin na cewa Amurkawan da ke yin tambayoyi ga wadanda ke tsare a Guantanamo sun wulakanta tsarkakakken littafin Musulmi Al-kura’ani mai girma. Shugaban majalisar hafsoshin rundunonin maya?an Amurka, janar Richard Myers ya fada a jiya alhamis cewa, masu bincike sun bi takardun bayanan yin tambayoyin sarai, amma ba su ga abun da ya tabbatar da sahihancin rahoton da mujallar Newsweek ta buga game da wulakanta Al-kura’ani ba.

XS
SM
MD
LG