Babbar kotun kasar Afirka ta Kudu, ATK, ta umurci gwamnati da ta biya diyya ga wani bature manomi wanda dubban mutane ’yan kama-wuri zauna suka mamaye gonarsa.
A cikin hukumcin da ta yanke yau jumma’a, kotun tsarin mulki ta Afirka ta kudu ta soki lamirin gwamnatin kasar a saboda kasa kare manoma daga irin wannan mamaya, tana mai bayyana mamayar a zaman sinadarin haddasa fitina.
Wannan kara dai wani bature manomi mai suna Braam Duvenhage shine ya shigar da ita. Mr. Duvenhage yayi shekaru 5 yana gwagwarmaya a kotu dangane da mamaye gonar iyalinsa dake Modderklip, kilomita 50 daga birnin johannesburg.
Hukumcin babbar kotun ya tabbatar da hukumce-hukumcen da kananan kotuna suka zartas na goyon bayan matsayin Mr. Duvenhage. Hukumcin bai kayyade yawan diyyar da gwamnati zata biya shi ba.